BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA
Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!Tambayoyi da amsarsu tare da
Mallam Ibrahim Zakzaky na arba'in
Menene matsayin dukan yara da ake yi a makaranta?
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam menene matsayin dukan yara da ake yi a makarantar boko a dalilin makara, surutu ko don rashin mai da hankali?
Daga Baballe Kwamanda Malam Madari 0802 794 5687
SHAIKH ZAKZAKY: Ana yi wa yara ladabi, amma akwai ka’ida na cewa abin da ya fi kada bulalar da za a yi masu ta wuce 5 zuwa 10. Kuma ya zama bulala ce kamar a hannu, ba kuma wanda zai yi masu tsanani ba. Wannan kuma ba lalai makarantun boko ba khasatan, duk gaba daya. Sai dai mukan ga wasu lokutan dukan ya zama ma wadansu Malamai tamkar al’ada ne, har ya tashi a ladabi ga yaro, wanda shi wannan ya kamata lallai a kawar da shi. Ya kamata ya zama in za yi wa yaro horo ya zama an yanke masa hukunci ne a kotun makaranta din. A ce an same shi da laifi kaza. Ba kawai in ya zo a dinga tsala masa bulala ba. Misali in ya yi wani laifi wanda makaranta ta hana, a kawo shi a tabbatar da hujjoji da shaidu a kan ya yi laifi, kuma a yanke masa hukunci a ce bulala uku, sannan kuma ya bayar da tafin hannunsa a fada masa rula a kwance, kuma ba da karfi ba. Ko a fyada masa hankici.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam menene matsayin musayar fata da tabarma a lokacin sallar lahiya da mutane ke yi?
Daga Musa Dahiru Ganye AD TS 080 0804 230 2810
SHAIKH ZAKZAKY: Ya halatta! Abin da muka sani shi ne ba a sayar da naman layya, akan ci ne a sadaukar. Amma ba fata yana bukatar ya yi amfani da ita wajen shimfida wa in ya so ko ya kyautar ko ya sadaukar ko kuma ya sayar din tunda ya ga tabarma ta fi masa amfani, sai ya bayar a ba shi tabarmarsa, ka ga ya sayar ya sayi tabarma kenan.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Allah ya gafarta Malam, ina da mata tana aiki a asibiti, kuma wani lokacin har suna kwana a wajen aikin. Yana halatta a gare ni na bar ta ta ci gaba da wannan aikin da take yi?
Daga Ja’afar Kaduna
SHAIKH ZAKZAKY: Tunda dai halatta kake batu ba wajibci bane. In ka ga ya yi maka, shi kenan. Sai mu ce in dai halacci ne ya halatta maka, in ka yarda. In ba ka yarda ba kuma sai ka nemi mara aikin asibiti. Ko kuma ta yi zamanta a gida ka biya ta albashi. Allahumma sai dai in aikin nata ya zama wajibi ne ga ceton rayukan al’umma wanda wata ba za ta iya tsayawa da wannan aikin in ba ita ba, to ta wannan fuskar ma ya wuce naka ikon.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam idan mutum Khumisi ya hau kansa ya fitar, sai dai kuma kafin ya kai ga mika wa masu shi, sai barayi suka sace, ya zai yi kenan? Zai sake fitarwa ne, ko kuwa wanda ya fitar da farko ya wadatar?
Daga Isma’il Sharif Zariya 0803 875 5850
SHAIKH ZAKZAKY: Ya danganta da inda aka sace din ne. Idan bayan ya fitar ne zai kai, yana kan hanya inda zai kai din, kuma lazim ne ya je wannan wurin ya kai, to shi kenan in aka sace shi ma’amuni ne. Sai da idan shi ne ya lizimta wa kansa kai shi wani wuri alhali zai iya bayarwa a kusa, to sai ya dauki takalifin wannan. Wannan haka yake ma a hukuncin zakka. Idan za ka iya ba wani a garin da kake, sai ka dauka za ka kai wani gari, sai ya salwanta a hanya kai za ka lamunce tunda bai zama maka lazim ka dauka ka kai can ba. Amma in bai fitar bane a cikin dukiyarsa sai aka sace har da dukiyar, to ya hau kansa. Amma in ya ware kafin ya mika, kuma ba sakaciya yi ba, to shi ma dai duk zai zama amintacce kenan, ba zai zama lazim ya sake fitarwa ba.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam ni dai babban soja ne kuma a baya mun yi wasu ayyuka marasa kyau a lokacin da muke wannan aikin, yanzu kuma na yi nadamar abubuwan da muka aikata, shi kenan ya wadatar da ni, ko kuwa akwai wasu abubuwa da da zan yi?
Daga wani dan uwa a Kaduna
SHAIKH ZAKZAKY: Tunda abubuwan da aka yi marasa kyau din an dunkule su, ba a san su wanne ne ba, idan hakkokin Allah ne, to neman gafara za ka yi. Kamar nadaman da ka yi, sai kuma ka nemi gafara shi kenan Allah ya yafe. Da fatan Allah ya yafe. Amma in ya yi ta’alluki da hakkokin wadansu mutane, to lallai su za a biya su hakkokinsu in zai yiwu, sawa’un a dukiyoyinsu ne ko a mutuncinsu, ka ga su akwai hakkinsu. In zai yiwu ka iya kubutar da kanka daga hakkokin wasu, musamman na dukiyoyi, to zai zama lazim ka yi haka. Sai dai in wanda ba kuma zai yiwu ba samsamsam, shi ma sai ka koma ga Allah da neman tuba.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam idan mutum ya tashi ba shi da abinci zai iya wucewa da azumi, kuma zai samu ladan wannan azumin da ya yi?
Daga Sani Muhammad Kaduna
SHAIKH ZAKZAKY: Eh na nafila haka yake. Idan mutum ya tashi da safe sannan ya ga cewa zai yi azumi ne ko don ba shi da abinci ko don ma saboda wane dalili yana iya yin azuminsa in dai bai ci komai ba. A nafila ana cewa hatta ma kafin faduwar rana, duk yana iya niyyar yin azumi. Amma idan a farali ne kamar na Ramadana shi ne in zawwal ba ta yi ba, bai ci komai ba kuma zawwal ba ta yi ba, to zai iya niyyarsa. Amma bayan zawwal ba zai wadatar da shi ba, duk da dai zai kama bakinsa, amma dai dole sai ya rama wannan azumin.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam da yake tafin hannun mace ba al’aura bane, yana halatta mutum ya yi musabaha da matar da ba muharramarsa ba?
Daga Alhaji Muhammad Suleja jihar Neja
SHAIKH ZAKZAKY: A’a ko da aka ce kallon sa bai haramta ba, to ba a ce kuma taban sa ba. Saboda haka taban jikinta bai halatta ba ta kowane hali. Inda ya halatta a gani kamar fuska da tafi ba kuma ya halatta a taba ne ba. Saboda haka musafaha da wadda take ba muharrama ba bai halatta ba.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam menene hukuncin yin dillanci a Musulunci?
Daga Aliyu Wanzam Giade jihar Bauci 0803 560 9463
SHAIKH ZAKZAKY: Halas ne matukar abin da ake ma dillancin ya halatta a sayar da shi. Da kuma sauran ka’idodi na shari’a a kan sha’anin ciniki, kamar misali dillancin nan zai yi a matsayin ana biyan sa lada ne ko an sayar ko ba a sayar ba? Wato kamar an suhurce shi kenan ya yi aikin sayarwa a biya shi, ko ya sayar ko bai sayar ba. Ko kuwa an ce ga shi nan ya sayar ne yana da wani kaso in ya sayar? Duk dai yadda aka yi. Wato dole ya zama tsarin dillancin ya yi daidai da shari’ar Musulunci. Ba mu ce duk dillanci ba kawai. Alal misali akwai abin da dillalai suka ce ma la’ada, wanda shi ba mu san shi ba a shari’a. Ka ga ba zai zama yana cin la’ada ba kenan sai dai ya ci lada. Kuma ba zai yi irin abin da dillan nan ba suke yi, musamman dillalan gida da gonaki wanda sukan rika baki biyu ba. Tsakanin mai saye da wanda ake sayar masa, ya rage kudi a nan, ya kara a can. Shi ya karbi kason da ya ma fi mai abin yawa.